logo

HAUSA

Amurka na daukar barazanar da Sin ke kawowa a matsayin dalilin fadada karfin sojanta a sararin samaniya

2024-01-26 20:21:51 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya bayyana cewa, kasar Amurka ta dade tana kara gishiri kan ra’ayin barazanar da Sin ke kawowa a fannin binciken sararin samaniya, don zargin kasar Sin ba tare da tushe ba, tare da daukar wannan ra’ayi a matsayin dalilin fadada karfin sojanta a sararin samaniya da kiyaye mulkinta a fannin aikin soja.

Wang Wenbin ya bayyana haka ne lokacin da yake tsokaci kan rahoton da Amurka ta gabatar game da yin takara a sararin samaniya.

Wang Wenbin ya jaddada cewa, kasar Sin ta tsaya tsayin daka kan manufar binciken sararin samaniya cikin lumana, da kin amincewa da yin takara a fannin aikin soja a sararin samaniya. Kana Sin ta yi kokarin sa kaimi ga kasa da kasa su yi shawarwari don cimma yarjejeniya bisa doka game da kayyade aikin soja a sararin samaniya da nufin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a sararin samaniyar. Har ila yau, Sin ta sake kalubalantar Amurka da ta daina yin bayanai ba tare da tushe ba, ta kuma dakatar da fadada aikin soja a sararin samaniya, haka kuma ta sauke nauyin da aka rataya a wuyanta. (Zainab)