logo

HAUSA

Ministan Harkokin Wajen Kasar Sin Zai Tattauna Da Mashawarcin Shugaban Amurka Kan Tsaro Yayin Ziyararsa A Thailand

2024-01-26 20:08:27 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar kasar Sin Wang Wenbin, ya ce dorewar tuntubar juna yadda ta dace tsakanin ministan harkokin wajen Sin Wang Yi da mashawarcin shugaban Amurka kan harkokin tsaro Jake Sullivan, wata muhimmiyar matsaya ce da shugabannin kasashen biyu suka cimma.

Wang Wenbin ya bayyana haka ne yau Jumma’a, lokacin da aka yi masa tambaya game da sabon zagayen tattaunawar da za a yi tsakanin manyan jami’an kasashen biyu a birnin Bangkok na kasar Thailand.

Kakakin ya kara da cewa, a yayin sabon zagayen tattaunawar, Wang Yi zai bayyana matsayar kasar Sin kan batun dangantakarta da Amurka da batun Taiwan, tare da musayar ra’ayi kan batutuwan da suka shafi duniya da na yankuna dake jan hankalin kasashen biyu. 

Bugu da kari, tattaunawar za ta gudana a Thailand ne saboda ziyarar da Wang Yi zai yi kasar daga yau Jumma’a 26 zuwa 29 ga watan Janairu, bisa gayyatar da mataimakin firaministan kasar Thailand, kuma ministan harkokin wajen kasar Parnpree Bahiddha-Nukara ya yi masa. (Fa’iza Mustapha)