logo

HAUSA

An kawo shawarar Najeriya ta yi koyi da matakan da kasar China ta bi wajen bunkasa ci gaba tare da martaba al’adu

2024-01-25 09:09:32 CMG Hausa

Shugaban jami’ar Abuja dake tarayyar Najeriya Farfesa Abdul-Rasheed Na’Allah ya ce, akwai bukatar Najeriya ta yi koyi da matakan da kasar Sin ta bi wajen samun nasarar ci gabanta.

Shugaban jami’ar ya bukaci hakan ne yayin wani taron bita da ofishin jakadancin kasar Sin a Najeriyaya ya shirya tare da hadin gwiwa da jami’ar ta Abuja a kan wayewar kan duniya. Ya ce, abun birgewa kasar ta China ba ta yi watsi da al’adunta ba a lokacin da take kokarin ci gaba.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Farfesa Abdul-Rasheed Na’Allah ya ci gaba da cewa, a matsayinta na kasa mafi yawan al’umma a duniya wadda take da sama da mutane biliyan guda, kasar China ta yi kokarin shiga sahun gaba a jerin kasashen duniya da suke da wayewa a fannonin ci gaba daban daban.

“Wajibi ne mu koyi da abun da kasar China ta yi wajen rungumar al’adun kasar. Da yawa wasu ’yan kasar ta China ba sa iya Turanci, to amma kuma kwazon aikinsu shi ne na farko a duniya. Yanzu ka je dakunan kimiyyar kasar Amurka za ka iske ’yan kasar China a wajen suna aiki amma ba sa jin Turanci. Waye ya gaya maka cewa Turanci shi ne mafita ga Najeriya? Yarukanmu suna kan gaba wajen warware halin da muke ciki. Duk al’ummar da ba ta yin wani tunani da yarenta babu yadda za a yi ta ci gaba.”

Da yake jawabi jakadan kasar China a Najeriya Mr Cui Jianchun ya tabbatar da cewa, a watan Oktoban wannan shekara ta 2024 za a gudanar da dandalin taro tsakanin China da kasashen Afrika.

“A don haka babban bikin za a yi shi ne a kasar China, kuma Najeriya za ta kasance cikin mahalarta, kuma jagoran wannan mahimmin taro. Kuma muna tunanin cewa za mu yi wani abu da ya shafi fito al’adu, a inda za a tura matasa zuwa kasar China daga Najeriya, inda za a shirya fim na hadin gwiwa da kuma rubutun adabi da za su fito da kyawawan al’adun Najeriya da kasar China. Akwai da yawa daga cikin matasan kasar China da ba su da sani sosai a kan al’adun Najeriya, wanda wannan zai bayar da damar matasan kasar ta Sin su fahimci al’adun Najeriya da kuma al’ummar kasar. Ina da yakinin cewa kasashen biyu za su yi aiki tare domin kawo canji.” (Garba Abdullahi Bagwai)