logo

HAUSA

Ministan Harkokin Wajen Sin Ya Gana Da Sakataren Majalisar Ministocin Kenya

2024-01-25 20:36:54 CMG Hausa

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya gana da sakataren majalisar ministoci kana ministan harkokin wajen kasar Kenya Musalia Mudavadi a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

Wang ya ce, tun bayan kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Kenya shekaru 60 da suka gabata, kasashen biyu sun kasance masu fahimta da goyon bayan juna, kana abokai na kwarai da suka amince da juna suke kuma hulda nagari, masu neman hadin gwiwar samun nasara tare. Shugabannin kasashen biyu sun kulla aminci da abokantaka, da ba da jagoranci bisa manyan tsare-tsare don raya dangantakar dake tsakanin kasashensu.

Da yake karin haske game da jawabin Wang, Mudavadi ya ce, hadin gwiwa a aikace a tsakanin kasashen Kenya da Sin, ya haifar da sakamako mai kyau, kuma raya shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya tare, ya taimaka matuka wajen raya tattalin arziki da ma kasar Kenya.

A madadin gwamnatin Kenya, Mudavadi ya jaddada cewa, kasarsa za ta ci gaba da bin ka'idar Sin daya tak a duniya, kana za ta tsaya tare da kasar Sin kan batutuwan da suka shafi yankin Taiwan da kare hakkin dan Adam, kuma kasar Kenya na fatan kara yin hadin gwiwa da kasar Sin.(Ibrahim)