logo

HAUSA

Dawo da huldar diflomasiya tsakanin Sin da Nauru ya sake tabbatar da manufar Sin daya ce tak a duniya

2024-01-24 18:53:37 CMG Hausa

Kasashen Sin da Nauru sun sake kulla huldar diflomasiya a tsakaninsu yau Laraba 24 ga wata. Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi da takwaransa na Nauru Lionel Rouwen Aingimea, sun tattauna a birnin Beijing, inda suka rattaba hannu kan wata sanarwar hadin gwiwa, kan dawo da huldar jakadanci tsakanin kasashen biyu ba tare da bata lokaci ba.

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya bayyana a yayin taron manema labaru na yau da kullum Larabar nan cewa, Nauru ta zama kasa ta 183 da ta kulla huldar diflomasiya da kasar Sin. Dawo da huldar diflomasiya tsakanin Sin da Nauru, ya sake tabbatar da cewa, kasar Sin daya ce tak a duniya, gwamnatin jamhuriyar jama'ar kasar Sin ita ce gwamnati daya tilo ta shari'a da ke wakiltar kasar Sin baki daya, kuma Taiwan wani yanki ne da ba za a iya raba shi da kasar Sin ba. Wannan wata shaida ce wadda ba za a iya musantawa ba, ita ma matsayar al'ummomin duniya da kuma ka'idoji na yau da kullun da aka amince da su wajen tafiyar da dangantakar ƙasa da ƙasa. (Ibrahim)