logo

HAUSA

Shugaban majalisar dokokin kasar Sin ya gana da takwaransa na kasar Djibouti

2024-01-24 11:13:18 CMG Hausa

Shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin Zhao Leji, ya gana da shugaban majalisar dokokin kasar Djibouti Dileita Mohamed Dileita, a ranar Talata a nan birnin Beijing.

Zhao ya ce, kasar Sin a shirye take ta zurfafa hadin gwiwa da kasar Djibouti a karkashin shirin “shawarar ziri daya da hanya daya” da kuma fadada hadin gwiwa a fannonin tashoshin jiragen ruwa, yankin cinikayya maras shinge, zuba jari da gina ababen more rayuwa.

Dileita a nasa bangaren ya ce, tun bayan kulla huldar diflomasiyya tsakanin Djibouti da Sin shekaru 45 da suka gabata, hadin gwiwa dake tsakanin kasashen biyu kan harkokin siyasa, da tattalin arziki, da al’adu, da more rayuwar jama’a ya samu sakamako mai kyau.

A ko da yaushe kasar Djibouti na tsayawa tsayin daka kan ka'idar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, kuma majalisar dokokin kasar Djibouti tana son karfafa mu'amalar abokantaka da takwararta ta kasar Sin, da yin musaya a harkokin majalisa, da ba da gudummawar majalisa wajen sa kaimi ga bunkasuwar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, a cewar Dileita. (Yahaya)