logo

HAUSA

Ya kamata a tsagaita bude wuta a zirin Gaza don kwantar da hankali a tekun Bahar Maliya

2024-01-24 20:21:01 CMG Hausa

Dangane da halin da ake ciki na baya-bayan nan a tekun Bahar Maliya, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Wang Wenbin ya bayyana a taron manema labarai na yau da kullum Larabar nan cewa, yanayin da ake ciki a tekun Bahar Maliya, wata babbar alama ce ta lalacewar rikicin Gaza, kuma abu mai muhimmanci, shi ne hanzarta dakile yakin Gaza. Kasar Sin ta yi kira ga dakatar da kai hari ga jiragen ruwan fararen hula, da kalubalantar bangarorin da abin ya shafa da su dakatar da tsananta yanayin da ake ciki a tekun Bahar Maliya, da tabbatar da tsaron hanyoyin jiragen ruwa a teku kamar yadda doka ta tanada. (Zainab)