logo

HAUSA

Najeriya da Indiya sun sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna game da sabbin hanyoyin samar da makamashi

2024-01-24 09:09:33 CMG Hausa

Najeriya ta sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna da kasar Indiya a game da bunkasa sabbin fasahohin samar da makamashi da kuma bayar da horo.

Ministan harkokin waje na Najeriya Ambassador Yusuf Maitama Tuggar ne ya sanya a madadin Najeriya yayin da takwaransa na kasar Indiya Mr. Subrah-Manyam Jaishankar ya sanya a madadin kasarsa .

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

An dai gudanar da bikin sanya hannu ne a ma’aikatar harkokin kasashen waje na Najeriya dake birnin Abuja, kuma bikin kulla wannan yarjejeniya yana daga cikin taro karo na 6 na hukumar hadin gwiwa tsakanin Najeriya da kasar Indiya wanda ya gudana a ranar Litinin da ta gabata karkashin jagorancin gwamnatin tarayyar Najeriya.

Haka kuma yarjejeniyar ta shafi sha’anin siyasa, al’adu, tsaro, harkokin sufurin jiragen sama da kuma batutuwan da suke da nasaba da ci gaban diplomasiyar kasa da kasa.

Ministan harkokin kasashen waje na tarayyar Najeriya Ambasada Yusuf Maitama Tuggar ya ce, daman can da jimawa akwai kwakkyawar alakar tsakanin kasashen biyu.

“Najeriya da kasar Indiya suna tarayya a kan abubuwa da dama, ta fuskar siyasa Najeriya ita ce kasa mafi girma da take bisa tafarkin demokradiyya a nahiyar Afrika yayin da kuma a yankin Asia kasar Indiya ke jan ragama, sannan kuma mu ne muka fi yawan jama’a, muna da alaka mai karfi kuma na dogon lokaci.”

Shi kuwa ministan harkokin kasashen wajen Indiya Mr Jaishankar bayan sanya hannu kan yarjejeniyar cewa ya yi, “Najeriya da kasar Indiya dukkanninmu muna fuskantar kalubalen kiwon lafiya. Ta yaya za mu samar da magunguna da kuma kayayyakin kiwon lafiya masu araha da kuma saukin samu ga jama’a, wannan na daya daga batutuwan da za mu iya duba a kansu.” (Garba Abdullahi Bagwai)