logo

HAUSA

Yawan ’yan kwadago dake kubuta daga kangin talauci ya kai miliyan 33.969 a kasar Sin

2024-01-24 10:52:36 CMG Hausa

Mataimakin shugaban ma’aikatar aikin noma da karkara ta kasar Sin Deng Xiaogang ya bayyana a yayin taron manema labarai da ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar ya gudanar a jiya Talata cewa, a shekarar bara, an samu sakamako mai inganci wajen kawar da talauci, kuma al’umma ba su sake komawa cikin talauci ba a cikin lokacin. Yawan ’yan kwadago dake kubuta daga kangin talauci ya kai miliyan 33.969, wanda ya zarce makasudin da aka tsara a bara wato miliyan 3.777.

A shekarar 2023, an kyautata tsarin yaki da talauci wajen tallafawa matalauta a wuraren kasar daban-daban, kuma a cikinsu fiye da kashi 60 cikin dari ba za su koma kangin talauci ba, yayin da aka sanya sauransu a cikin matakan tallafawa. Deng ya bayyana cewa, a shekarar bana, ma’aikatar aikin noma da karkara za ta inganta karfin bunkasuwar wuraren dake kawar da kangin talauci da kubutar da al’ummun daga kangin talauci a shekarar bana.

Ya bayyana cewa, za a inganta tsarin hada masana'antu na karkara da aikin noma domin baiwa mutanen da aka fitar da su daga kangin talauci damar samun karin fa'ida a masana'antu. Karfafa hadin gwiwar ’yan kwadago a tsakanin yankunan gabas da yamma, da yin amfani da tarukan taimakon guraben aikin yi, da wuraren jin dadin jama'a, ayyukan agaji da sauran hanyoyi don tabbatar da cewa yawan guraben aikin yi ga mutanen da suka fita daga kangin talauci ya kasance fiye da miliyan 30. (Safiyah Ma)