logo

HAUSA

Xi ya gana da firaministan Antigua and Barbuda

2024-01-24 20:01:50 CMG Hausa

A yau ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da firaministan kasar Antigua da Barbuda Gaston Browne a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

Xi ya yi nuni da cewa, har kullum Gaston Browne yana mai da hankali matuka kan raya dangantakar da ke tsakaninsa da kasar Sin, da tsayawa tsayin daka kan ka'idar Sin daya tak, kana yana goyon bayan kasar Sin kan batutuwan da suka shafi moriya da muhimman batutuwan dake shafarta, abubuwan da ya yaba matuka. A bisa yanayi da ake ciki, kasar Sin na son karfafa hadin gwiwa da dabarun raya kasa da Antigua da Barbuda, tare da ingiza karin nasarori a huldar dake tsakanin kasashen biyu, domin samun moriyar jama'ar kasashen biyu.

A nasa bangare Brown ya bayyana cewa, kasar Sin ta gabatar da shirin raya kasa, da shirin raya wayewar kan duniya, da shirin samar da zaman lafiya a duniya, wanda ke da nufin sa kaimi ga bunkasuwar wadata da zaman lafiya a dukkan kasashen duniya, kuma wadannan ra’ayoyi sun samu karbuwa matuka a duk fadin duniya. Ana fatan sauran kasashe, musamman kasashe masu tasowa, za su bi sahun kasar Sin, tare da gina duniya mai zaman jituwa tare da sa kaimi ga samun ci gaban duniya cikin adalci. (Ibrahim)