logo

HAUSA

Kasar Sin za ta ci gaba da tabbatar da ikonta

2024-01-24 20:12:52 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya musanta sanarwar da kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Vietnam ya bayar, ya kuma yi nuni da cewa, tsibiran Paracel da Nansha, yankin kasar Sin ne, wadanda ke da shaidu na tarihi da kuma doka. Sin ce ta fara ganowa tare da saka musu suna da aiwatar da ayyuka a tsibiran, kuma ta ci gaba da iko a kansu. A ko da yaushe kasar Sin tana adawa da ikirarin da kasashen da abin ya shafa ke yi kan kasar Sin ba bisa ka'ida ba, kuma za ta ci gaba da tabbatar da ikonta. (Zainab)