logo

HAUSA

Mai Da Jama’A A Gaban Komai, Jigon Tsarin Raya Birnin Fuzhou

2024-01-23 11:36:06 CMG HAUSA

DAGA CMG

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da shirin raya birnin Fuzhou na tsawon shekaru 20 mai lamba 3820 a shekarar 1992 yayin da yake mukamin sakataren kwamitin JKS na birnin. Inda ya mai da muradun jama’a a gaban komai yayin da ya tsayar da manufofin raya birni da kiyaye muhalli da aikin ba da ilmi da al’adu da sauransu.

A cikin shekaru 30 da suka gabata, birnin na ci gaba da yin riko da tunaninsa, don daga matsayin zaman rayuwar jama’a.

Gidajen kwana muhimman moriya ne ga jama’a, suna da alaka da zaman rayuwa har ma raya birnin, wanda an dade ana mai da hankali kan wannan batu bisa tsarin 3820. Ban da wannan kuma, Xi Jinping ya bayyana cewa, dole ne a raya tattlin arziki tare da kiyaye muhalli, ba za a iya raba su ba.

A shekarar 1995, Xi Jinping ya shaidawa manema labarai cewa, aikin da ya fi gamsar da shi, shi ne aikin gamsar da jama’a. Ya ce, yana gamsar da ayyukan da aka tabbatar dake da alaka da zaman rayuwa da zamantakewar jama’a. (Amina Xu)