logo

HAUSA

Girgizar kasa mai karfin maki 7.1 ta afku a jihar Xinjiang ta kasar Sin

2024-01-23 14:03:42 CMG Hausa

Cibiyar kula da girgizar kasa ta kasar Sin (CENC) ta sanar da cewa, girgizar kasa mai karfin maki 7.1 ta afku a gundumar Wushi na lardin Aksu da ke jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta a arewa maso yammacin kasar Sin da misalin karfe 2:09 na safiyar yau Talata.

Cibiyar ta bayyana cewa, wurin da girgizar kasar ta afku na da nisan kilomita 50 daga gundumar Wushi, kuma akwai kauyuka biyar masu nisan kilomita 20 kewaye da wurin.

Wasu gidaje da wuraren kiwon dabbobi ne suka ruguje a yankin, yayin da wasu makiyayan suka samu kananan raunuka, kamar yadda majiya daga yankin ta bayyana.

Bayan afkuwar girgizar kasa, rundunar kashe gobara ta gundumar Wushi ta aika da tawagar mutane 10 ta gaggawa zuwa yankin da lamarin ya shafa. Kaza lika, ma’aikatan kashe gobara na lardin Aksu, sun tattara mutane 60 domin isa yankin da girgizar kasar ta afku. (Muhammed Yahaya)