logo

HAUSA

Kasar Sin ta fitar da takardar bayani kan tsarin doka da matakan yaki da ta’addanci

2024-01-23 12:55:05 CMG Hausa

A yau Talata ne ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya fitar da wata takardar bayani mai taken “tsarin doka da matakan yaki da ta’addanci na kasar Sin.”

Takardar ta bayyana ta’addanci a matsayin abin ki ga dukkan bil’Adama, wanda ke haifar da babban barazana ga zaman lafiya da tsaro na kasa da kasa, kuma ya kasance kalubale ga dukkan kasashe da dukkan bil’Adama, ya zama dole dukkan kasashen duniya su yaki da ta’addanci. 

A shekarun da suka gabata, kasar Sin ta bullo da hanyar yaki da ta'addanci bisa dokar da ta dace da hakikaninta ta hanyar kafa tsarin doka mai inganci, da sa kaimi ga aiwatar da doka mai tsauri, bisa rashin son kai, da tabbatar da gudanar da adalci ba tare da nuna son kai ba, da kiyaye hakkin dan Adam yadda ya kamata, a cewar takardar.

Takardar aikin ta kara da cewa, yayin da ake kiyaye ra'ayin al’ummar duniya mai makomar bai daya, kasar Sin a shirye take ta yi hadin gwiwa da sauran kasashe don ciyar da harkokin yaki da ta'addanci gaba a matsayin wani bangare na gudanar da harkokin duniya. (Yahaya)