logo

HAUSA

Sin tana son ci gaba da yin hadin gwiwa da kasa da kasa wajen yaki da ta’addanci

2024-01-23 19:36:30 CMG Hausa

Ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin, ya fitar da wata takardar bayani mai taken “tsarin doka da matakan yaki da ta’addanci na kasar Sin” a yau, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya bayyana game da wannan batu cewa, Sin tana son ci gaba da yin hadin gwiwa tare da kasa da kasa wajen yaki da ta’addanci, da shiga ayyukan yaki da ta’addanci na duniya, da yin koyi da mu’amala da juna bisa tushen girmamawa da nuna adalci ga juna, da sa kaimi ga raya sha’anin yaki da ta’addanci na duniya, da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankunan duniya.

A gun taron manema labaru na yau da kullum Talatar nan, Wang Wenbin ya bayyana cewa, a matsayinta na wadda ta taba fuskantar illar ta’addanci, kasar Sin ta dade tana fuskantar barazanar ta’addanci. A cikin shekaru da suka gabata, kasar Sin ta yi cikakken bayani kan dokoki, da halaye, da aikinta na yaki da ta'addanci, da koyi daga wasu kasashe, da tsara wata hanyar yaki da ta’addanci bisa doka dake dacewa da yanayin kasar, hakan ya tabbatar da tsaron kasa, da na zamantakewar al’umma, da kuma tsaron rayuwa da dukiyoyin jama’ar kasar, kana ta samar da gudummawa wajen tabbatar da tsaro a duniya da yankuna baki daya. (Zainab)