logo

HAUSA

Sin za ta kara kaimi ga farfado da tattalin arzikin duniya

2024-01-22 19:57:43 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, Sin za ta maida hankali ga bukatun kasuwa, da kiyaye samar da dama a harkokin ciniki da zuba jari a duniya, da kara sa kaimi ga farfado da tattalin arzikin duniya.

Wang Wenbin ya bayyanawa ‘yan jarida cewa, wani rahoton da cibiyar nazarin harkokin yawon shakatawa ta kasar Sin ta fitar a kwanakin baya, na nuna cewa, a yanayin sanyi na biyu bayan gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta Beijing, yawan mutane da suka je yawon shakatawa dake nasaba da kankara tun daga lokacin sanyi na shekarar 2023 zuwa na shekarar 2024 zai zarce miliyan 400, yawan kudin shiga da aka samu daga wannan fanni a kasar Sin, zai kai Yuan biliyan 550. A sakamakon karuwar tattalin arziki a yayin ranakun bukukuwan Sin da kuma fannin kankara, zai taimaka ga raya kasuwar yawon shakatawa ta duniya, hakan ya shaida karfin Sin na raya tattalin arziki. (Zainab)