logo

HAUSA

Shugaban kasar Sin ya ba da umarnin ceton mutanen da suka bace a zaftarewar kasa ta kudu maso yammacin kasar

2024-01-22 14:20:58 CMG

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bukaci a yi iyakacin kokarin gano tare da ceto mutanen da suka bace a zaftarewar kasa da ta afku a gundumar Zhenxiong dake birnin Zhaotong na lardin Yunnan da ke kudu maso yammacin kasar Sin.

Xi, ya ba da umarnin ne bayan zaftarewar kasa da ta afku a gundumar a safiyar yau Litinin.

Mahukuntan yankin sun ce mutane 47 sun makale bayan da kasa ta zaftare ta binne gidajensu a safiyar ranar Litinin a birnin na Zhaotong.

Hukumomin kula da bala’o’i na lardin sun fara aikin ba da agajin gaggawa tare da tura masu aikin ceto da dimbin injunan kashe gobara da sauran kayayyakin aiki.

Fiye da mutane 200 ne aka kwashe cikin gaggawa daga yankin. (Yahaya)