logo

HAUSA

An tabbatar da mutuwar mutane 7 bayan zaftarewar kasa da ta auku yankin kudu maso yammacin Sin

2024-01-22 20:45:47 CMG Hausa

Rahotanni na cewa, an gano mutane 7 da aka tabbatar sun mutu ya zuwa karfe 6 da mituna 30 na yammacin yau, biyo bayan zaftarewar kasa da ta auku a lardin Yunnan dake kudu maso yammacin kasar Sin, kamar yadda hukumomin yankin suka bayyana.

Hedkwatar bayar da agajin gaggawa ta yankin ta sanar da cewa, iftila’in zaftarewar kasa ta afku ne a kauyen Liangshui da ke birnin Zhaotong da misalin karfe 6 na safiyar yau, inda mutane 47 suka bace.

Bayanai a cewa, ma'aikatan ceto 795 dake aiki da jirgi mara matuki da motoci 120 da suka hada da na'urorin tonon kasa, da kuma motocin sufuri, suna gudanar da aikin bincike da ceto a wurin. (Ibrahim)