logo

HAUSA

Sin tana son yin aiki tare da abokan huldar kasa da kasa don tallafawa Comoros wajen kiyaye zaman lafiya

2024-01-22 19:45:32 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya bayyana cewa, kasarsa tana son yin aiki tare da abokan huldar kasa da kasa, don tallafawa kasar Comoros wajen kiyaye zaman lafiyar al'umma, da taka rawa mai kyau wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaban kasar.

Rahotanni sun bayyana cewa, tun bayan da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar Comoros ta sanar a ranar 16 ga watan Janairu cewa, shugaban kasar mai ci Azali Assoumani ne ya lashe zagayen farko na babban zaben kasar, jama’a suka fito kan tituna a sassa da dama a kasar suna zanga-zanga, yayin da kasashen Amurka da kasashen Tarayyar Turai da Faransa suka fitar da sanarwa, inda suka nuna shakku kan sakamakon zaben.

Dangane da wannan batu, Wang Wenbin ya bayyana cewa, zaben shugaban kasa lamari ne na cikin gida na kasar Comoros, kuma a ko da yaushe kasar Sin tana kiyaye ka'idar rashin tsoma baki a harkokin cikin gidan kasashe, da mutunta ra'ayi da zabin jama'ar Comoros. (Ibrahim)