logo

HAUSA

Liu Guozhong ya halarci taron kolin kasashen kudancin duniya karo na 3 inda ya gabatar da jawabi

2024-01-22 17:10:49 CMG Hausa

Wakilin musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping, kana mamban hukumar siyasa na kwamitin kolin Jam’iyyar Kwaminis ta Kasar Sin, kana mataimakin shugaban majalisar gudanarwar kasar Liu Guozhong, ya halarci taron kolin kasashen kudancin duniya karo na 3 a Kampala wato babban birni na kasar Uganda, inda ya gabatar da jawabi.

Liu Guozhong ya bayyana cewa, bana shekara ce ta cika shekaru 60 da kafuwar kungiyar kasashe 77 wato G77. A cikin shekaru 60 da suka gabata, kasashe masu tasowa sun kasance kan turbar mutunta juna, amincewa da juna, cimma moriyar juna da kuma taimakawa juna. Game da kasashe masu tasowa, dogaro da kansu shi ne tushen siyasa, samun karfi ta hadin kai shi ne al’adar gargajiya, bunkasuwa da farfadowa shi ne manufar tarihi, kuma adalci shi ne bukatarsu.

A halin yanzu, yanayin duniya a cikin shekaru 100 da suka gabata ya sauya cikin sauri, kasashe masu tasowa suna fuskantar yanayi mai tsanani. Kamata ya yi mu sake fara binciken hanyar zamanantarwa, inganta hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa, shiga aikin yin kwaskwarimar tsarin mulkin duniya, zurfafa dangantakar abokantaka ta ci gaban duniya ta hanyar hadin kai, daidaito, da moriya ga kowa. (Safiyah Ma)