logo

HAUSA

Yawan kunshin sakonni da aka yi jigilarsu a kasar Sin ya kai biliyan 132.07 a shekarar 2023

2024-01-22 14:01:32 CMG Hausa

Bisa kididdigar da hukumar kula da harkokin sakonni ta kasar Sin ta fitar a yau Litinin, yawan kunshin sakonni da aka yi jigilarsu a kasar Sin a shekarar bara, wato shekarar 2023 ya kai biliyan 132.07, wanda ya karu da kashi 19.4 cikin dari bisa makamancin lokaci na shekarar 2022.

A barar har ila yau, yawan kunshin sakonni da aka yi jigilarsu a yankin gabas na kasar ya kai kashi 75.2 cikin dari, kuma a yankin tsakiyar kasar, ya kai kashi 16.7 cikin dari, yayin da ya kai kashi 8.1 cikin dari a yankin yammacin kasar. Bisa makamancin lokaci na shekarar 2022, yawan kunshin sakonni da aka yi jigilarsu a yankin gabas ya ragu da kashi 1.6 cikin dari, yayin da a yankin tsakiya, ya karu da kashi 1 cikin dari, sannan a yankin yamma ya karu da kashi 0.6 cikin dari. (Safiyah Ma)