logo

HAUSA

Xi ya rattaba hannu kan yadda za a fito da ka’idojin da aka yi wa kwaskwarima kan dokokin aikin soja

2024-01-22 19:38:12 CMG Hausa

Shugaban kwamitin kolin sojan kasar Sin Xi Jinping, ya rattaba hannu kan wata doka, wadda za ta fito da wasu ka'idojin da aka yi wa kwaskwarima kan dokokin da suka shafi aikin soja, wadanda za su fara aiki a ranar 1 ga Maris.

Wata sanarwa da aka fitar Litinin din nan na cewa, ka’idojin da suka kunshi sassa 85 cikin babi 13, da aka yi wa kwaskwarima, za su daidaita tsarin aiki da hanyoyin aiwatar da dokokin soja bisa sabuwar dokar da aka yi wa kwaskwarima.

Sanarwar ta ce, dokokin da aka yi wa kwaskwarima na da matukar ma'ana ga kokarin da ake na kara inganta dokokin da suka shafi aikin soji, da inganta aiwatar da dabarun tafiyar da aikin soji bisa doka, da kuma karfafa tsarin tafiyar da harkokin aikin soja daga dukkan fannoni. (Ibrahim)