logo

HAUSA

An kammala bitar wasan kwaikwayo karo na biyu na shirye-shiryen bikin sabuwar shekarar Sinawa na 2024

2024-01-22 11:02:16 CMG Hausa

An kammala bitar wasan kwaikwayo na shirye-shiryen bikin sabuwar shekarar Sinawa na 2024 da babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG ya gudanar a jiya Lahadi. 

A karon farko, an yi bitar wasan kwaikwayo tsakanin kananan dandaloli hudu dake birnin Shenyang na lardin Liaoning, da birnin Changsha na lardin Hunan, da birnin Xi'an na lardin Shaanxi, da kuma birnin Kashgar na jihar Xinjiang, tare da babban dandalin da aka kafa a birnin Beijing. Yanayi mai dadi ya mamaye ko'ina, wanda ya nuna sabon yanayi na sassa daban-daban na kasar Sin na ci gaba a kan sabuwar tafiya.

A yayin bitar wasan kwaikwayon karo na biyu, tsarin musamman da kirkirar shirye-shirye na kowane karamin dandali yana nuna al'adun gida masu wadata da yanayin sabuwar shekara, yana ba mutane masu farin ciki daga ko'ina a duniya damar samun haduwa mai ban sha’awa. (Safiyah Ma)