logo

HAUSA

Cin zalin da 'yan siyasar Amurka ke yi yana kara muni

2024-01-22 20:26:18 CMG Hausa

Dangane da batun "barazanar kasar Sin", da ‘yan siyasar Amurka ke ta yadawa, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya bayyana a gun taron manema labaru na yau da kullum Litinin din nan cewa, yaudarar cin zarafi da 'yan siyasar Amurka da abin ya shafa ke yi na kara yin tsanani.

Wang Wenbin ya ce, daga zargin da ake yi na cewa, na'urorin fasahar sadarwa na kasar Sin sun bar baya da kura, da ikirarin cewa kugiyar daga kaya da kasar Sin ta kera, wai na’urorin tattara bayanan sirri ne, da mayar da batiran motoci masu amfani da wutar lantarki da kasar Sin ke kerawa a matsayin barazana ga tsaron kasa. Maganar "barazanar da kasar Sin ke haifarwa" da 'yan siyasar Amurkan da abin ya shafa na kara ta'azzara, a lokaci guda kuma, manufarsu ta hakika ta dakile ci gaban kasar Sin ta hanyar fakewa da batun tsaron kasa na kara fitowa fili. Abin da 'yan siyasar Amurka ke yi cin zarafi ne tsantsa. (Ibrahim)