logo

HAUSA

Sin ta yaba da kokarin kasashe ‘yan ba ruwanmu wajen ciyar da zaman lafiya gaba a duniya

2024-01-21 19:56:59 CMG Hausa

Wakilin musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping, Liu Guozhong, ya halarci taron kolin kungiyar kasashe ‘yan ba ruwanmu karo na 19 da aka gudanar daga ranar Juma'a zuwa jiya Asabar a birnin Kampala na kasar Uganda. A jawabin da ya gabatar, ya bayyana muhimmiyar rawar da kungiyar ke takawa wajen ciyar da bukatar zaman lafiya da ci gaban bil-adama a duniya.

Liu, mataimakin firaministan kasar Sin, kana mamba a ofishin siyasa na kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya bayyana cewa, kungiyar NAM, wadda aka kafa ta a lokacin da ake tsaka da yunkurin 'yantar da kasashe a nahiyar Asiya, da Afirka da kuma Latin Amurka, ta samu ci gaba matuka wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaban bil-adama a duniya.

Ya bayyana cewa, kamata ya yi a ci gaba da martaba 'yancin kai, da nuna adawa da siyasar neman suna, da neman daidaito tare da kawar da bambance-bambance, da samar da zaman lafiya, da neman ci gaba ta hanyar hadin kai, da kokarin samar da ci gaba tare, da bayar da shawarar samun daidaito, da adalci. (Ibrahim)