logo

HAUSA

GDPn Beijing ya kai kusan Yuan triliyan 4.4 a shekarar 2023

2024-01-21 15:33:34 CMG Hausa

Magajin garin birnin Beijing na kasar Sin, Yin Yong ya bayyana yayin da yake gabatar da rahoton aikin gwamnati a taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar birnin cewa, GDPn birnin ya kai kudin kasar Sin kusan Yuan triliyan 4.4 kwatankwacin dalar Amurka biliyan 618.26 a shekarar 2023, wanda ya karu da kashi 5.2 bisa dari kan na shekarar 2022

Rahoton ya bayyana cewa, kudaden kasafin kudin jama'a na birnin, ya zarce Yuan biliyan 600 a shekarar 2023, wanda ya karu da kashi 8.2 bisa dari kan na shekarar 2022. Alkaluman na nuna cewa, adadin marasa aikin yi a birni a bara, ya kai kashi 4.4 bisa 100.

Haka kuma, kididdigar farashin kayayyakin masarufi na birnin, bai sauya ba a shekarar 2023. Karuwar kudin shiga na mazauna birnin, ya ci gaba da habaka tattalin arzikin kasar a bara, yayin da alamomi daban-daban kamar GDP na kowane yanki, da ingancin ma'aikata ya kasance mafi girma a tsakanin lardunan kasar baki daya. (Ibrahim)