logo

HAUSA

An rantsar da Tshisekedi a matsayin shugaban DRC

2024-01-21 16:17:37 CMG Hausa

Shugaban jamhuriyar Demokuradiyyar Kongo, Félix-Antoine Tshisekedi Tshilombo ya yi rantsuwar kama aiki a birnin Kinshasa a jiya, inda ya fara wa’adin shugabancinsa karo na biyu na shekaru 5.

A yayin bikin, shugaba Tshisekedi ya godewa tawagar kiyaye zaman lafiya ta MDD, bisa gudummawar da ta bayar wajen samar da zaman lafiya a kasar a shekarun baya-bayan nan, kana ya bayyana cewa, za a kara gina ayyukan more rayuwa a kasar a nan gaba, da raya tattalin arziki a fannoni daban daban, da kuma zafafa yaki da kungiyoyin dake dauke da makamai dake gabashin kasar

A ranar 9 ga wannan wata ne, kotun kundin tsarin mulkin kasar DRC ta yanke hukuncin amincewa da ingancin sakamakon zaben shugaban kasar da aka yi a ranar 20 ga watan Disamba na shekarar bara, kuma shugaban kasar Tshisekedi ya samu zarcewa a karo na biyu.(Zainab)