logo

HAUSA

Gwamnatin Najeriya: kamfanonin hakar ma’adanai na taka rawa ga ci gaban tattalin arziki kasar

2024-01-21 15:33:33 CMG Hausa

Ma’aikatar bunkasa harkokin ma’adanai na tarayyar Najeriya ta tabbatar da cewa, kamfanonin hakar ma’adanai dake kasar suna taka mahimmiyar rawa ga ci gaban tattalin arzikin kasa duk da kalubalen da bangaren ke cin karo da su.

Karamin minista a ma’aikatar Alhaji Uba Mai-gari ne ya tabbatar da hakan a Ilorin ta jihar Kwara dake arewa ta tsakiyar Najeriya yayin babban taron shekara karo na 5 na majalissar kasa a kan bunkasa sana’ar hakar ma’adanai da sauran albarkatu.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Abdullahi ya aiko mana da rahoto. 

 

Alhaji Uba Mai-gari ya ce, Allah ya horewa Najeriya da tarin albarkatun kasa, amma abun takaici a wasu lokuta sana’ar hakar ma’adanai na cin karo da matsaloli daban daban, kama daga rashin kayan aiki na zamani, rashin tabbas na cinikin ma’adanan a kasuwar duniya da karuwar haramtattun kamfanonin hakar ma’adanai.

Ministan ya yi kira ga mahalarta taron wadanda suka hadar masu hakar ma’adanai da masu sarrafa ma’adanan, da masu saka jari da masana masu nazarin bincike da kuma sauran masu ruwa da tsaki da su hada kai wajen baiwa gwamnati gudummawa a kokarinta na farfado da masana’antar sarrafa karafa.

“Farfado da kamfanonin sarrafa karafa dake Najeriya muhimmancinsa bai tsaya kawai ga bangaren ci gaba tattalin arziki ba, muhimmancinsa ya shafi kasa baki daya ne domin kuwa zai bijiro da kafofin ayyukan yi, samar da al’umma mai dogaro da kai, a don haka bai dace ba mu janye jiki daga kalubalen dake gabanmu.”

Karamin ministan ma’adanan Najeriya ya kara yi kira ga masu hakar ma’adanai da su rinka hada kai da al’umomin yankunan da ake hakar ma’adanan ta hanyar tabbatar da ganin suna amfana daga irin nau’ikan albarkatun da ake samu a yankunansu, inda ya ce ta yin hakan ne kawai masu wannan sana’a za su samu nasarar da suke bukata. (Garba Abdullahi Bagwai)