logo

HAUSA

Sudan ta dakatar da zama mamba a kungiyar IGAD

2024-01-21 15:44:26 CMG Hausa

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sudan ta sanar a jiya Asabar cewa, kasar ta dakatar da kasancewa mamba a kungiyar raya kasashen gabashin Afirka wato IGAD.

A cikin wata sanarwa da ma'aikatar ta fitar ta bayyana cewa, shugaban majalisar rikon kwaryar kasar Abdel Fattah Al-Burhan, ya sanar da shugaban zaman kungiyar IGAD shawarar da Sudan ta yanke ta dakatar da zama mamba a kungiyar.

A cewar sanarwar, matakin na Sudan ya biyo bayan rashin mutunta shawarar da Sudan ta yanke, wadda aka mika mata a hukumance, ta dakatar da hulda da kungiyar kan duk wani batu da ya shafi Sudan, wanda bai faru ba a babban taron kolin na IGAD da aka gudanar a Uganda ranar Alhamis.

A makon da ya gabata ne dai, Sudan ta bayyana rashin amincewarta da taron kungiyar IGAD da aka shirya a ranar 18 ga watan Janairu a Kampala, babban birnin Uganda, domin tattauna halin da ake ciki a Sudan, tana mai cewa, abin da ke faruwa a Sudan, batu ne na harkokin cikin gidan kasar. (Ibrahim)