logo

HAUSA

Rundunar ’yan sandan Najeriya ta kaddamar da dakarun tunkari matsalar garkuwa da mutane a Abuja

2024-01-20 10:37:26 CMG Hausa

Sefeton janaral na ’yan sandan Najeriya Mr. Olu-kayode Egbetokun ya jagoranci bikin kaddamar da dakarun musamman da za su tunkari ayyukan masu garkuwa da mutane da hare-haren ta’addanci a birnin Abuja da yankunan da suke kewaye da birnin.

Daga cikin ayyukan dakarun na musamman, sun hada da yin sintiri a tsakanin garuruwan da suke da iyaka da birnin Abuja da kuma kara sanya ido a kan masu hada-hada a cikin kwaryar birnin.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Daman dai tun a cikin shekarar bara ta 2023 rundunar ’yan sandan ta Najeriya ta sanar da bayar da horon musamman ga ’yan sanda dubu 40 wanda kuma bayan kammala samun horon za a tura su jihar Katsina da wasu jihohi 9 na kasar ciki har da birnin Abuja.

Sefeton ’yan sanda na tarayyar Najeriya Mr Olu Kayode haka kuma ya tabbatar da cewa, kwamandojin da za su jagoranci wadannan rundunoni na musamman za su samu horo ne a kasar Mexico wanda za a tura su zuwa wadannan jihohi guda 10.

“Bisa ga kokarin cimma kudurce-kudurcenmu, nake farin cikin sanar da kaddamar da kashi na farko na rundunar musamman wanda wani sashe ne daga cikin rundunar ’yan sanda ta kasa, kuma rundunar ta kunshi ’yan sandan da suka sami horo na musamman, sannan kuma an tanadar musu kayan aiki da ababen hawa, wadannan dakaru su ne za su rinka kai dauki na dakile duk wasu hare-haren da sauran abubuwan dake barazana ga yanayin tsaro a birnin Abuja da kewaye. Lamarin da yake haifar da firgici a zukatan al’umma, wannan runduna dai ba wai an samar da ita ne ba rana tsaka ba, a’a daman can akwai tsarin samar da ita da jimawa a kokarin da ake yi na sake fasalin harkokin tsaro a Abuja, hedikwatar mulkin kasar.”

Sefeton ’yan sandan na Najeriya ya ce, jihohi 27 ne aka tsara tura wadannan dakarun musamman bayan jihohi 10 da aka fara da su, kuma an zartar da hakan ne bayan rahoton dake nuna cewa jahohin su suka fi samun yawan fuskantar barazanar tsaro. (Garba Abdullahi Bagwai)