logo

HAUSA

Wang Yi Ya Gana Da Takwaransa Na Cote Di’voire

2024-01-19 10:41:25 CMG HAUSA

 

Jiya ne, mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya tattauna da takwarasa na kasar Cote d'Ivoire, Kacou Houaja Léon Adom a birnin Abidjan.

Yayin tattaunawar, ministocin kasashen biyu sun yi magana mai kyau, game da dangantakar abokantaka da hadin gwiwa ta dogon lokaci dake tsakanin kasashen biyu, inda suka bayyana cewa, za su ci gaba da nuna goyon baya ga juna kan batutuwan da suka shafi muhimman moriyarsu.

Yana mai cewa, kasarsa za ta ci gaba da martaba manufar Sin daya tak a duniya, kuma Taiwan wani yanki ne da ba za a iya raba shi da kasar Sin ba. Kazalika, bangarorin biyu na fatan kara hadin kai da samun moriyar juna, kasar Cote Di’voire ta yaba da irin gagarumin goyon bayan da kasar Sin ke baiwa gasar cin kofin kwallon kafan nahiyar Afirka karo na 34 dake gudana a kasar.

Haka kuma, bangarorin biyu sun tattauna kan yadda za su kara hada kai da yin ciniki tsakaninsu da halin da ake ciki a yammacin Afrika da manyan batutuwan kasa da kasa dake jawo hankalinsu.

Bayan shawarwarin, ministocin harkokin wajen kasashen biyu sun kuma shaida hadin gwiwa wajen rattaba hannu kan takardar mika motocin bas masu aiki da wutar lantarki guda 6 da na’urorin caji guda 3 da gwamnatin kasar Sin ta ba wa gwamnatin Cote Di’voire, domin amfani da su a gasar wasan kwallon kafa na kasashen Afirka. (Amina Xu)