logo

HAUSA

Kasar Sin na fatan kara sa kaimi ga bunkasuwar dangantakarta da kasashen Afirka

2024-01-19 22:42:46 CMG

A ranar Alhamis ne ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya kammala ziyararsa a kasashen Masar, Tunisia, Togo, da Cote d'Ivoire. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana a yayin taron manema labarai na yau cewa, ziyarar ta ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ta ci gaba da kiyaye al’adar ziyarar farko ta ministan harkokin wajen kasar Sin zuwa Afirka a kowace shekara.

Mao Ning ta bayyana cewa yayin wannan ziyarar, ministan harkokin waje Wang Yi ya yi tattaunawa mai zurfi tare da bangaren Afirka game da dangantakar bangarorin biyu da manyan batutuwan kasa da kasa da na shiyya-shiyya da suka shafi moriyar juna, da cimma manyan matsaya, da kara amincewar da juna ta fuskar siyasa, da inganta mu’amala da hadin gwiwa a fagage daban-daban.

Mao Ning ta bayyana cewa, za a gudanar da sabon taron dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka a kasar Sin. Kasar Sin za ta yi aiki tare da kasashen Afirka wajen kaddamar da matakan hadin gwiwa da suka dace da bukatun raya kasa na Sin da Afirka a sabon zamani, tare da ingiza sabbin kuzari kan gina al'umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya ga Sin da Afirka. (Yahaya)