logo

HAUSA

Yawan kudaden dake shafar masana’antun kasar Sin ya kai matsayin koli a duniya a cikin shekaru 14 a jere

2024-01-19 14:28:38 CMG HAUSA

 

Yau Juma’a da safe, ofishin yada labarai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya gudanar da taron manema labarai don bayyana halin bunkasuwar masana’antu da sadarwa a shekarar 2023 a nan kasar Sin.

A gun taron, wani jami’i ya bayyana cewa, tattalin arzikin masana’antu na samun bunkasuwa yadda ya kamata, sana’ar bayanai da sadarwa na samun ci gaba cikin sauri da inganci.

A shekarar 2023, yawan bunkasuwar masana’antu ya karu da kashi 4.6% bisa na shekarar 2022. Ban da wannan kuma, muhimman sana’o’i 10 da manyan larduna 10 masu karfi a fannin masana’antu sun ba da tabbaci ga bunkasuwa a wannan fanni. Yawan kudaden dake shafar masana’antu ya kai matsayin koli a duniya a cikin shekaru 14 a jere. (Amina Xu)