logo

HAUSA

Jami’ar Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira da a samar da agajin gaggawa don magance rikicin Nijar

2024-01-19 19:56:12 CMG

A cikin wani kira na gaggawa da aka yi a ranar Alhamis, wata babbar jami’a ta Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci kasashen duniya da su kara tallafawa Nijar, kasar da ke fama da matsaloli masu dimbin yawa.

Edem Wosornu, darektar ayyuka da bayar da shawarwari a ofishin kula da ayyukan jin kai na MDD (OCHA) ta yi karin haske game da halin kaka ni ka yi da ake ciki a Nijar, ta kafar bidiyo daga Yamai babban birnin kasar.

Wosornu ta jaddada halin da kusan mutane miliyan 4.3 ke ciki a Nijar, wadanda fiye da rabinsu yara ne, da ke fama da "rikici, bala'o'i da sauyin yanayi, da yunwa, da annoba."

Ta ce, yunkurin jin kai na MDD a Nijar na bukatar kusan dalar Amurka miliyan 662, amma kalubalen kudade da matsalolin isa ga al'ummar da abin ya shafa su ne manyan cikas. (Yahaya)