logo

HAUSA

Ma’aikatar tsaron Najeriya ta bukaci ’yan kasar da su daina biyan kudin fansa ga masu garkuwa da mutane

2024-01-19 09:03:18 CMG Hausa

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta gargadin al’ummar kasar da su daina tara kudi ta hanyar neman tallafin jama’a a kafofin sada zumuntar zamani domin biyan kudin fansa ga masu garkuwa da mutane.

Ministan tsaron kasar Alhaji Badaru Abubakar ne ya bukaci hakan yayin wata ganawar da ya yi da manema labarai a birnin Abuja. Ya ce yin hakan haramun ne kuma yana sanyawa mutane su zama malalata wajen neman halal.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Ministan ya jaddada wannan bukata ce ga al’ummar Najeriya biyo bayan rahoton sace wasu iyalai 7 da aka yi a birnin Abuja inda ake neman miliyan 60 zuwa miliyan 100 a matsayin kudin fansa kafin a sako su, wannan ya sanya ’yan uwan mutanen fara neman tallafin kudi daga wajen jama’a ta hanyar kafofin sada zumunta domin biyan bukatun masu garkuwa da mutanen.

Alhaji Badaru Abubakar ya ce, duk da dai masu garkuwa da mutane sun halaka uku daga cikin wadancan iyalai, amma wannan ba zai zama hujjar tara kudin domin sako ragowar ba, kasancewar jami’an tsaro daban-daban na iya bakin kokarin ganin sun kwato su.

Mininstan tsaron tarayyar Najeriya ya alakanta karuwar garkuwa da mutane da ake samu yanzu haka a birnin Abuja bisa yadda jami’an tsaro suka hana wadannan ’yan ta’adda sakewa a jihohin dake shiyyar arewa ta tsakiyar Najeriya da kuma arewa ta yamma.

“Dukkanmu mun san cewa akwai dokar da take aiki a halin yanzu wadda ta haramta biyan kudin fansa, amma abun takaici mutane suna amfani da kafofin intanet da gidajen rediyo wajen neman jama’a su bada gudummawar kudi domin biyan kudin fansa, wanda wannan ba abun da zai haifar illa sake dagula al’amura, ya dace mu daina biyewa masu neman wannan agaji.” (Garba Abdullahi Bagwai)