logo

HAUSA

Angola na samar da ganga miliyan 1.098 na danyen mai a kullum a shekarar 2023

2024-01-19 10:45:40 CMG Hausa

Alkaluman hukuma na nuna cewa, kasar Angola tana samar da kusan ganga miliyan 1 da dubu 98 na danyen mai a kowace rana a shekarar 2023, inda ta kasance kasa ta uku dake samar da mafi yawan man fetur a Afirka, bayan kasashen Najeriya da Libya.

Rahoton kasuwar mai na wata-wata da kungiyar kasashe masu arzikin man fetur ta OPEC ta fitar a ranar Larabar da ta gabata, ya daina sanya kasar Angola a cikin jadawalin bayanan da suka shafi mai na kasashe mambobin kungiyar, tun bayan sanarwar da kasar ta fitar na ficewa daga kungiyar ta OPEC a ranar 21 ga watan Disamban bara.

A nahiyar Afirka, kasashen Najeriya da Libya ne kadai ke da matsakaicin yawan hako mai a rana fiye da Angola a shekarar 2023,inda Najeriya ke hako ganga miliyan 1 da dubu 234 yayin da Libya ke hako ganga miliyan 1 da dubu 189 a kowace rana, bi da bi.(Ibrahim)