logo

HAUSA

Manzon musamman na shugaba Xi Jinping na kasar Sin zai halarci bikin rantsar da shugaban Liberia

2024-01-19 15:59:09 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta sanar a yau cewa, bisa gayyatar da gwamnatin kasar Liberia ta yi, manzon musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping kuma mataimakin shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama’ar kasar Sin Ba Te’er zai halarci bikin rantsa da shugaban kasar Liberia Joseph Nyumah Boakai da za a yi a ranar 22 ga wannan wata a birnin Monrovia, fadar mulkin Liberia. (Zainab Zhang)