logo

HAUSA

Bunkasuwar Sin Za Ta Ingiza Farfadowar Duniya

2024-01-18 16:09:14 CMG HAUSA

DAGA MINA

Yau Laraba, kasar Sin ta gabatar da alkaluman bunkasuwar tattalin arzikinta. Bisa kididdigar da Sin ta gabatar, GDPn kasar a shekarar 2023 ya kai RMB Yuan fiye da triliyan 126, wanda ya karu da kashi 5.2 bisa dari idan an kwatanta da shekarar 2022. Ban da wannan kuma, adadin ya fi hasashen da aka yiwa duk duniya wanda ya kai kashi kimanin 3%. Hakan ya sa, Sin tana sahun gaba a fannin karuwar tattalin arziki a duniya, yawan rawar da za ta taka ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya zai kai fiye da kashi 30%, ta zama jigo mai karfi a duniya a wannan fanni.

Abin lura shi ne, Sin tana samun ci gaba a zo a gani a fannin kirkire-kirkire da kimiyya da fasaha, asusun fasahar sadarwa da krikire-kirkire na Amurka ta gabatar da jerin suanayen sana’o’in dake da muhimmanci matuka a wannan fanni, guda 7 daga cikinsu a kasar Sin suna matsaya daya a duniya.

Idan an henge nesa kan nakomar tattalin arziki a shekarar 2024, hasashen karuwar tattalin arzikin kasar Sin da IMF da kamfanin Goldman Sachs sun yi su ne kashi 4.6% da 4.8%. A sabon shekara, Sin na da karfi sosai wajen tabbatar da samun bunkasuwa mai dorewa, har ma za ta kawowa duk fadin duniya kuzari da zarafi bisa bunkasuwarta da kirkire-kirkiren da za ta yi. (Mai tsara da rubutu: MINA)