logo

HAUSA

Sin da Cote d'Ivoire za su fadada hadin gwiwa a tsakaninsu

2024-01-18 19:59:18 CMG

Shugaban kasar Cote d'Ivoire Alassane Ouattara ya gana da ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi da ke ziyarar aiki a birnin Abidjan a jiya Laraba, inda bangarorin biyu suka yi alkawarin zurfafa hadin gwiwa a tsakaninsu.

A yayin ganawar, Ouattara ya yaba da hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu, inda ya bayyana cewa kasar Sin ta zama babbar abokiyar cinikayya mafi girma da kuma tushen zuba jari ga kasar ta Cote d’Ivoire. 

Cote d'Ivoire za ta ci gaba da ba da fifiko wajen raya dangantakar dake tsakaninta da kasar Sin, a cewar shugaban.

Ya kuma jaddada cewa kasar Sin daya ce tak a duniya, kuma Taiwan wani yanki ne na kasar Sin.

Wang ya ce, bangaren kasar Sin na matukar yabawa irin goyon bayan da Cote d'Ivoire ke baiwa kasar Sin wajen kiyaye dinkuwar kasar da cikakkun yankunanta. Ya kuma bayyana cewa, kasar Sin a shirye take ta sa kaimi ga inganta hadin gwiwar moriyar juna tsakaninta da Cote d'Ivoire.

Ya ci gaba da cewa, kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da kasashen Afirka, wajen gano ingantattun hanyoyin da suka dace da yanayin da kasashen ke ciki, da kiyaye 'yancin kansu, da samar da ci gaba da wadata tare, ta yadda za a cimma nasarar zamanantarwa tare.

Wang ya kuma tattauna da ministan harkokin wajen Cote d'Ivoire a ranar Larabar.

Kasar Cote d'Ivoire ita ce kasa ta karshe a Afirka na ziyarar farko da ministan harkokin wajen kasar Sin ya kai a ketare a bana. Wang ya kuma ziyarci Masar da Tunisiya da kuma Togo yayin ziyarar da ta fara a ranar Asabar. (Yahaya)