logo

HAUSA

Li Qiang ya gana da firaministan kasar Ireland

2024-01-18 10:38:11 CMG Hausa

Jiya Laraba, firaministan kasar Sin Li Qiang ya gana da takwaransa na kasar Ireland Leo Varadkar a gidan saukar baki na gwamnati dake Dublin na kasa ta Ireland.

A yayin ganawarsu, Li Qiang ya bayyana cewa, tun bayan kulla huldar diplomasiyya tsakanin Sin da Ireland yau shekaru 45 da suka gabata, dangantakar dake tsakanin kasashen biyu ta samu ci gaba mai inganci yadda ya kamata. Musamman a ’yan shekarun nan, bisa hangen nesa na jagorancin hangen nesa na shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na Ireland Michael D Higgins, dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da Ireland na kara zurfafa a tsakaninsu, kuma ana ci gaba da kara yin mu'amala da hadin gwiwa a fannoni daban daban, wanda ya kawo fa'ida a zahiri ga jama'ar kasashen biyu.

Kasar Sin tana son yin hadin gwiwa tare da Ireland, don ci gaba da sada dadadden zumuncin dake tsakaninsu, da karfafa amincewar juna a fannin siyasa, da zurfafa hadin gwiwar moriyar juna, da kara samun cikakken damar samun ci gaba, da samun moriya tsakanin kasashen biyu da ma jama'arsu.

A nasa bangare, Leo Varadkar ya ce, kasar Sin muhimmiyar abokiyar hadin gwiwar kasar Ireland ce, kuma kasashen biyu na ci gaba da mutuntawa da amincewa da juna. Ireland ta yaba da manyan nasarorin da kasar Sin ta cimma a fannin tattalin arziki da zamantakewa, ta kuma martaba ka'idar kasancewar Sin daya tak a duniya a ko da yaushe kamar yadda ta saba, tana kuma fatan kasar Sin za ta cimma burinta na samun dunkulewar kasar baki daya cikin lumana. Kana, kasarsa tana fatan habaka harkokin zuba jari da mu’amalar al’adu a tsakanin kasashen biyu. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)