logo

HAUSA

Kumbon Tianzhou-7 ya hade da tashar sararin samaniyar Sin

2024-01-18 13:09:11 CMG Hausa

Hukumar kula da harkokin sararin samaniya ta kasar Sin (CMSA) ta bayyana cewa, kumbon Tianzhou-7 na kasar Sin, ya kammala daidaitawa, tare da hadewa da tashar binciken sararin samaniya ta Tiangong yau Alhamis.

A cewar hukumar CMSA, kumbon Tianzhou-7 ya yi nasarar hadewa da muhimman sashen Tianhe ne da karfe 1 da mituna 46 na safe, agogon birnin Beijing.

Bayanai na cewa, ma'aikatan kumbon Shenzhou-17 dake cikin tashar sararin samaniya, za su shiga cikin kumbon, tare da jigilar kayan dake cikinsa kamar yadda aka tsara. (Ibrahim)