logo

HAUSA

Shugaban Togo ya gana da ministan harkokin wajen Sin

2024-01-18 10:16:53 CMG Hausa

Shugaban kasar Togo Faure Essozimna Gnassingbé, ya gana da mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi dake ziyara a kasar jiya Laraba a birnin Lome.

A yayin ganawar, shugaba Faure ya yi karin haske kan dangantakar dake tsakanin Togo da Sin da ma hadin gwiwarsu, ya ce bisa dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka, kasar Togo da sauran kasashen Afirka, sun samu babban ci gaba a fannin samar da kayayyakin more rayuwa. Ya kara da cewa, tattalin arzikin Afirka ya kara bunkasa, an kuma tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a nahiyar Afirka, har ma al’ummun nahiyar na smaun Moriya. Wadannan suna da nasaba da tallafin da kasar Sin ta dade tana samarwa. Togo ta yaba da yadda kasar Sin ke tabbatar da adalci a duniya, da nuna adawa da tsoma baki a harkokin cikin gidan Afirka, da taka rawar da ta kamata wajen samun ci gaban Afirka cikin lumana.

A nasa bangare, minista Wang Yi ya isar da gaisuwar shugaban kasar Sin Xi Jinping ga shugaban kasar Togo, inda ya bayyana cewa, zumuntan dake tsakanin Sin da Togo, ya zama abin misali ga hadin gwiwar dake tsakanin kasashe masu tasowa. Sin za ta kara yin hadin gwiwa tare da kasar Togo kan manyan tsare-tsare, da nuna goyon baya ga kasar Togo wajen samun bunkasuwa mai dorewa. Ya ce, karni na 21, karni ne na farfado da kasashe masu tasowa. Kasar Sin za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka tare da kasashen Afirka, da taimakawa kasashen Afirka wajen gaggauta samun ci gaba kansu, da sa kaimi da inganta hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka, da kara amfana da sakamakon hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka, don samun moriyar Togo da kasashen Afirka.

A wannan rana kuma, Wang Yi ya yi tattaunawa tare da firaministar kasar Togo Mme Victoire Sidémeho Tomégah Dogbé da kuma ministan harkokin wajen kasar Togo Robert Dussey. (Zainab Zhang)