logo

HAUSA

Kasar Sin ta harba kumbon dakon kaya domin aikewa da kayayyaki ga tashar sararin samaniya

2024-01-17 23:03:58 CMG Hausa

Hukumar kula da sararin samaniya ta kasar Sin ta sanar da cewa, a daren Larabar nan ne kasar Sin ta harba kumbon Tianzhou-7 da ke dakon kaya, domin kai kayayyakin da za a yi amfani da su a tashar sararin samaniya ta Tiangong.

Roka kirar Long March-7 Y8 dauke da kumbon Tianzhou-7, ya tashi ne daga wurin harba kumbon Wenchang dake lardin Hainan a kudancin kasar Sin a ranar Larabar nan.

Wannan dai shi ne aikin jigilar kaya na biyu tun bayan da tashar sararin samaniyar kasar ta shiga cikin matakin aikace-aikace da ci gaba. Idan aka kwatanta da Tianzhou-6, an kara inganta karfin lodin Tianzhou-7. Kayayyakin da ke cikin kumbon Tianzhou-7 ya hada da kayayyakin rayuwa da tufafi da abinci ga 'yan sama jannati. (Yahaya)