logo

HAUSA

Firaministan kasar Sin: Ya kamata Sin da Ireland su yi aiki tare don tabbatar da cinikayya cikin 'yanci da bude kofa

2024-01-17 23:17:41 CMG Hausa

Firaministan kasar Sin Li Qiang dake ziyara a kasar Ireland ya bayyana a yau Laraba cewa, ya kamata kasashen Sin da Ireland su yi aiki tare don kiyaye tsarin cinikayya na kasa da kasa cikin 'yanci da bude kofa, da kiyaye tsarin samar da kayayyaki na masana'antun duniya.

Li ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake ganawa da shugaban kasar Ireland Michael D. Higgins a Aras an Uachtarain, fadar shugaban kasar ta Ireland. (Yahaya)