logo

HAUSA

Ma’aikatar harkokin wajen Sin: Zabar kasuwar kasar Sin ba hadari ba ne dama ce

2024-01-17 21:01:43 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta bayyana a yau Laraba 17 ga wata cewa, zabar kasuwar kasarta, ba hadari ba ne, akasin haka, dama ce. Kasar za kuma ta kara fadada bude kofarta ga kasashen waje.

Firaministan kasar Sin Li Qiang ya halarci taron shekara-shekara na dandalin Davos wato dandalin tattauna tattalin arzikin duniya na bana, inda ya yi jawabi yana mai cewa, akwai alakar tattalin arziki ta kut da kut tsakanin kasashen duniya. Rarrabuwar kawuna zai iya haifar da illa ga tattalin arzikin duniya. Kasar Sin na ganin cewa, ya dace a girmama ka’idojin sana’o’in kasa da kasa, da tsayawa tsayin daka wajen kawo sauki da kawar da cikas ga harkokin kasuwanci da zuba jari, da ci gaba da karfafa hadin-gwiwa domin cimma moriya tare, al’amarin da zai dace da muradun bangarori daban-daban.

Mao Ning ta kuma jaddada cewa, a matsayin kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya, kasar Sin ta kan bayar da gudummawar kaso 30 bisa dari ga habakar tattalin arzikin duniya a ‘yan shekarun nan, abun da ya sa ta zama muhimmin karfi ga ci gaban duk duniya. A halin yanzu, Sin na himmatuwa wajen zamanantar da kanta ta hanyar samar da ci gaba mai inganci, al’amarin da zai kara sanya kuzari ga bunkasar tattalin arzikin duniya. Jami’ar ta ci gaba da cewa, kasarta za ta tsaya ga fadada bude kofa ga kasashen waje, ta yadda sauran kasashe za su iya cin gajiyarta. (Murtala Zhang)