logo

HAUSA

Firaministan Kasar Sin Na Ziyarar Aiki A Ireland

2024-01-17 10:25:51 CMG Hausa

Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya bayyana dangantakar dake tsakanin kasashen Sin da Ireland a matsayin wadda ke da kyakkyawar makoma da dimbin damarmaki.

Li Qiang ya bayyana hakan ne bayan saukarsa a filin jirgin saman Dublin na Ireland a jiya Talata, inda ya samu tarba daga ministan kula da muhalli da yanayi da sadarwa kuma ministan sufuri na kasar Eamon Ryan da kuma jakadan Sin a Ireland He Xiangdong.

A bana za a cika shekaru 45 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Ireland. A cewar Li Qiang, cikin shekaru 45 da suka gabata, Sin da Ireland sun rungumi ka’idar mutunta juna da samun daidaito a tsakaninsu, lamarin da ya zama misali na kyakkyawar hulda da hadin gwiwar moriyar juna tsakanin kasashe masu mabambantan tarihi da al’adu da tsarin siyasa.

Ya kara da cewa, a shekarun baya-bayan nan, karkashin muhimmin jagoranci da hadin gwiwar shugabannin kasahen biyu, Sin da Ireland sun raya amincinsu da hadin gwiwa a fannoni da dama, wadanda suka samar da kyawawan sakamako.

Li Qiang ya isa Ireland ne bayan halartar taron shekara-shekara na dandalin tattauna tattalin arzikin duniya na bana, tare da ziyarar aiki a kasar Switzerland. (Fa’iza Mustapha)