logo

HAUSA

GDPn kasar Sin ya karu da 5.2% a shekarar 2023

2024-01-17 14:00:03 CMG HAUSA

 

Yau Laraba da safe, ofishin yada labarai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta shirya taron manema labaru, inda ya bayyana yadda tattalin arzikin Sin ya gudana a shekarar bara. Bisa kididdigar da aka yi, GDPn kasar a shekarar 2023 ya kai RMB Yuan fiye da triliyan 126, wanda ya karu da kashi 5.2 bisa dari idan ba a yi la’akari da hauhawar farashi ba.

A sa’i daya kuma, alkaluman farashin kayayyakin masarufi na CPI ya karu da kashi 0.2% bisa na shekarar 2022.

Ban da wannan kuma, yawan hatsin da kasar Sin ta girba ya kai fiye da tan miliyan 695, wanda ya karu da tan miliyan 8.88, kwatankwacin kashi 1.3%. (Amina Xu)