logo

HAUSA

Li Qiang ya taya Gabriel Attal murnar zama firaministan Faransa

2024-01-17 11:23:01 CMG HAUSA

 

Firaministan kasar Sin Li Qiang ya taya Gabriel Attal murnar kama mukamin firaministan kasar Faransa.

Yayin tattaunawarsu ta wayar tarho, Li Qiang ya ce, a bana ake cika shekaru 60 da kafuwar huldar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu, kuma dangantakarsu ta shiga wani sabon mataki da za su ci gaba da raya ta, ta yadda za ta zama mai karin kuzari a nan gaba. Ya kara da cewa, Sin na fatan kara hada kai da Faransa don zurfafa mu’ammala da hadin gwiwa a bangarori daban-daban, ta yadda za su taka rawa wajen kafa huldar kasashen biyu mai dorewa da samar da moriyar juna, bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni. (Amina Xu)