logo

HAUSA

Firaministan Sin ya gana da shugabar kwamitin kungiyar EU

2024-01-17 10:50:51 CMG Hausa

Firaministan kasar Sin Li Qiang ya gana da shugabar kwamitin kungiyar EU Ursula von der Leyen a yayin taron shekara-shekara na dandalin tattaunawa kan tattalin arzikin duniya na shekarar 2024 a garin Davos.

A yayin ganawar da aka yi a jiya, Li Qiang ya bayyana cewa, Sin tana daukar aikin zurfafa dangantakarta da kasashen Turai a matsayin aikin diplomasiyya mai muhimmanci, kana tana son hada hannu da bangaren Turai wajen aiwatar da ayyukan da shugabannin Sin da Turai suka cimma daidaito kansu, da inganta dangantakar dake tsakanin Sin da Turai bisa ka’idojin fahimta da girmama juna, ta yadda za a sa kaimi ga samun bunkasuwa da wadata a tsakaninsu, har ma a duk duniya baki daya.

A nata bangare, Ursula von der Leyen ta bayyana cewa, bangaren Turai na yabawa kasar Sin kan yadda ta kara bude kofarta ga kasashen waje, kana ba muradin katse hulda da kasar Sin. Ta kara da cewa, Turai na son kara yin mu’amala da kasar Sin, da zurfafa hadin gwiwarsu a fannonin tinkarar sauyin yanayi, da sa kaimi ga yin kwaskwarima kan tsarin kungiyar WTO, da kara yin mu’amalar al’adu, don kai dangantakar dake tsakanin Turai da Sin zuwa wani sabon matsayi. (Zainab Zhang)