logo

HAUSA

NIPA: Sin ta mallaki kusan miliyan 5 na ingantattun ikon mallakar fasaha

2024-01-16 15:11:35 CMG Hausa

Hukumar kula da hakkin mallakar fasaha ta kasar Sin NIPA ta bayyana a yau Talata cewa, adadin ingantattun hakkin mallakar fasaha a kasar Sin ya zarce miliyan 4.99 ya zuwa karshen shekarar 2023.

Mataimakin shugaban hukumar ta NIPA Hu Wenhui ya bayyana yayin wani taron manema labarai cewa, adadin ingantattun lambobin shaidar fasaha a kasar Sin ya kai miliyan 46.15, inda ya bayyana ci gaban da kasar Sin ta samu a shekarar 2023 a fannin ikon mallakar fasaha.

Ya kara da cewa, an ba da izinin ikon mallakar fasaha guda dubu 921 a shekarar 2023, yayin da aka shigar da bukatar neman ikon mallakar fasaha na kasa da kasa kusan 74,000 ta hanyar yarjejeniyar hadin gwiwar ikon mallaka. (Yahaya)